Majalisar Dattawa Ta Yi Alhinin Mutanen Makaranta da Aka Sace a Oyo da Borno, Ta Bukaci Daukar Matakin Gaggawa
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya nuna matuƙar damuwa kan sace malamai da ɗalibai da ‘yan bindiga suka yi a Jihar Oyo, da kuma sache yara a Borno tare da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace. Akpabio ya yi wannan kira a ranar Talata yayin da Majalisar Dattawa ta koma zaman aiki a ranar 2 ga Yuni, 2026, bayan hutun makonni huɗu wanda ya bai wa sanatoci damar komawa mazabunsu da kuma halartar zaɓen fidda gwani na jam’iyyunsu. A cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Anietie Ekong, ya fitar, an rawaito Sanata Akpabio yana gaya wa ‘yan majalisar cewa yana baƙin cikin yadda Majalisar ke komawa aiki cikin yanayin jimami. Ya ce: “Abokai da abokan aiki, muna komawa bakin aikinmu ne a ƙarƙashin inuwar wani mummunan al’amari da ya girgiza ƙasarmu. “Sace yara ‘yan makaranta da malamai a Jihar Oyo da kuma Borno ba kawai hari ne kan fararen hula ba; hari ne a kan mu baki ɗaya. “Muna jimami domin idan ba za mu iya kare ‘ya’yanmu ba, to muna jefa makomarmu cikin haɗari. Muna jimami domin ƙasar da ba za ta iya tabbatar da tsaron malamanta ba, tana raunana ginshiƙa ilimi da ake dogaro da su. “Kuma muna jimami domin muddin waɗannan yara suna hannun masu garkuwa da mutane, ƙasarmu ma tana cikin wani irin yanayin da be dache ba. “A yau, muna alhinin rasuwar malamai biyu masu sadaukarwa: Mista Michael Oyedokun, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane, da kuma Mista Adesiyan Adegboye, wanda ya rasa ransa a lokacin harin. “Muna kuma jimamin yaron da rayuwarsa ta ƙare tun kafin ya samu damar cika alkawarin da rayuwarsa ke ɗauke da shi. Muna tare da iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu cikin wannan raɗaɗi. Rashinsu namu ne. Baƙin cikinsu namu ne. Zafinsu namu ne.” Sai dai ya tabbatar da cewa, ta hanyar ƙoƙarin gwamnati da hukumomin tsaro, za a kuɓutar da waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane cikin aminci, sannan a haɗa su da iyalansu. Akpabio ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da kada su mayar da batun tsaron ƙasa wata hanyar siyasa, sai dai su haɗa kai wajen yaƙi da ‘yan bindiga da ta’addanci. Ya ce: “A irin waɗannan lokuta, akwai jarabar rarrabuwa, zargin juna, da neman anfani daga masifa. “Dole ne ‘yan siyasa da masu neman muƙamai su guji irin wannan neman suna mai arha. Waɗanda ke sace yaranmu, suna addabar al’ummominmu, kuma suna kashe fararen hula marasa laifi, ba sa bambance jam’iyya, addini ko ƙabila. “Harinsu yana kan Najeriya ne gaba ɗaya. Saboda haka, martaninmu dole ne ya dace da girman ƙalubalen. Dole ne mu kasance cikin haɗin kai, ƙarfi da jajircewa. “Mu ci gaba da goyon bayan duk wata halastacciyar hanya da ta zama dole wajen ƙarfafa tsaro, kare makarantunmu, kare al’ummominmu, da kuma tabbatar da cewa kowane ɗan bindiga ya fuskanci cikakken hukuncin shari’a.” Ya ƙara da cewa: “A madadin Majalisar Dattawa ta Tarayyar Najeriya, ina miƙa ta’aziyyarmu mai zurfi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, al’ummar makarantar da abin ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar Jihar Oyo da Borno.”












